Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta tabbatar da cewa ta kammala duk wasu shirye-shirye na gayyatar wasu gwamnoni da wa’adin mulkin su ya kare.

 

Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa ne ya tabbatar da hakan a wata ganawa da Daily Trsut ta yi dashi a ranar Alhamis.

 

Bawa ya bayyana cewa hukumar za ta fara gayyatar gwamnonin ne a ranar 29 ga watan Mayu 2023.

 

A yayin tattaunawar Bawa bai ayyana sunayen gwamnoni da za su gayyata ba,sakamakon wa’adin mulkin su bai kammala ba.

 

Shugaban ya kara da cewa dokar kasa ba ta bayar da damar kama wani shugaban kasa ko gwamna ba da ya ke kan karagar mulki sai dai bayan karewar wa’adin mulkinsa.

 

Abdulrasheed Bawa ya ce bayan shirin kama gwamnoni akwai wasu ma’aikatun gwamnati biyu da hukumar ta ke tsaka da bincike akan su bisa zargin yin wadaka da kudade.

 

Bawa ya bayyana cewa a daya daga cikin ma’aikatun anyi almundahanar naira biilyan hudu na wasu kwangiloli 20 ta hanyar amfani da ma’aikata wajen buga takardun bogi.

 

Shugaban ya ce a halin yanzu su na ci gaba da gudanar da bincike akan ma’aikatun guda biyu tare da biyan su kudade har sau biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: