Babban bankin kasa Najeriiya CBN ya bai wa bankunann kasar umarnin su gudanar da aiki a yau Asabar da kuma Gobe Lahadi domin bayar da takardun naira da alumma ke nema.

Kamar yadda sanarwa ta fito daga babban bankin na kasa wato CBN a shafinsa na twitter ya ce ya na mai umartar bankunan kasuwanci da su gudanar da aiki a yau Asabar da Lahadi domin a wadata yan Najeriya da takardun kudi da su ka yii karanci.

Ya ce ya bai wa dukkanin bankunan kasuwanci ishashshen takardun naira wadanda za su wadaci mutane domin amfanin alamarun yau da gobe tare da umarni su sanya kudade a a cikin injin cirar kudi na ATM.

Sanarawan ta ce yin hakan zai sa kudade su wadatu a hannun mutane don su ci gaba da alamuran yau da kulum.

idan ba manta ba a shekarar bara ne babban bankin kasa CBN ya bijiro da tsarin sauya fasalin wasu daga cikin takardun kudin kasar, inda jama a su ka yi ta ce-ce-ku-ce akan sha’anin wanda hakan ya kai ga wasu daga cikin gwamnonin Najeriya sun shigar da kara akan sauyin kuma su kayi nasara akai.

dalilin da yasa banki CBN ya sakarwa yan Najeriya mara domin su ci gaba da amsar tsaffin takardu da kuma daina fama da karancin naira a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: