Wasu da ake zargin yan garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa wani malamin addinin kirista a jihar kaduna.

kamar yadda shugaban kungiyar kirstoci ta CAN na jihar Joseph Hayab ya ce an yi garkuwa da faston coci ne a yayin da yake yankin sa a jihar Kaduna.

Sannan ya ce an saki wasu daga cikin mutane 100 da yan garkuwa a suka sa ce a kwanakin baya da suka gabata a cewar Joseph hayab.

kuma ya ce an yi garkuwa da fastoci uku kafin zabe amma an saki biyu daga ciki.

sannan suna ci gaba da bin hanyoyin da ya kamata don kubutar da wanda yake hannun yan bindigar yanzu haka.

cikin bayanansa ya ce yan garkuwan sun nemi a ba su naira miliyan 50 duk da dai sun daidata akan miliyan biyar domin fansa.

sai dai rundunar yan sandan jihar kaduna bata ce komai game da lamarin garkuwar ba

Leave a Reply

%d bloggers like this: