Akalla yan cirani 36 ne suka rasa rayaukansu yayin ketare tekun birinin Sfax dake kasar Tunusiya.
kamar yadda rahotanni suka bayyana sun ce akalla mutane sama da 60 ne ba a gani ba a yayi da jirgin ruwan su ya nitse a cikin ruwa
cikin wadanda ake zargin ruwa ya hallaka akwai kananan yara da jarirai maza da mata wadanda aka tafi da su ciranin.
Suma jami’an bakin gabar taken sun bayyana cewa akalla jirage sama da 50 suka dakatar wadanda suke so su tsallaka tekun zuwa kasar Italiya daga kasashen Afrika.
sannan wannan shi ne kifewar jirgin karo na biyar a cikin kwanaki biyu a yankin.
Ga mai sauraron labarai zai ji lokaci zuwa lokaci mutane daga kasashen afrika suna tafiya kasashen turai cikin jirgin don neman abun duniya wanda a wasu lokutan ya kan kai ga rasa rayukansu a ruwan koma a harbe su tun da sun shiiga ba bisa ka ida ba.
Irin wannan matsalar dai ana samun ta ne daga mutane yan kasashen Afrika irinsu Najeriya Nijer kamaru da chadi da dai sauran kasashen kewaye.
Baya ga haka masana na ci gaba da fadakarwa kan cewa yin hakan sabawa doka ne ake yi mutum ya kai ga hallaka ransa da na sauran alumma.


