Ƙungiyar ƴan sakai ta Najeriya tayi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, da ya sanya hannu kan dokar kafa hukumar ƴan sakai kafin zuwan ranar 29 ga watan Mayu lokacin da zai bar kan karagar mulki.

A cewar ƙungiyar, majalisar tarayya tuni ta amince da kuɗirin kafa hukumar VGN (Establishment) Bill 2022.

Rahoton jaridar Punch ya nuna yadda Babban kwamandan ƴan sakan, Dr Usman Jahun, ya bayyana buƙatar hakan a birnin Abeokuta ta jihar Ogun yayin tattaunawa da ƴan jarida lokacin da ya kai ziyara kan ƴaƴan ƙungiyar a yankin Kudu maso Yamma.

Ya ce majalisar wakilai da majalisar dattawa duk sun amince da ƙudirin dokar.

Abinda kawai suke jira shine sa hannun shugaban kasa.

Jahun ya bayyana cewa amincewa da ƙungiyar a hukumance zai samar da ayyukan yi sannan zai sanya jami’an sa-kai su cike giɓin rashin isassun jami’an tsaron da ake fama da su a ƙasar nan.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: