Kwamandan ƙungiyar ƴan ta’addan ISWAP, Abu Muhammed, ya halaka mataimakin sa, Abu Darda, a dalilin barin da yayi sojoji suka farmaki sansanin su a ƙauyukan Mukdolo da Bone.

Farmakin na sojojin dai ya sanya an halaka mayaƙan ƙungiyar 41 ciki har da Abu-Zahra Munzir.

Zagazola Makama wani masani kan lamuran tsaro a yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa fusataccen kwamandan ya hallaka Abu Darda ne a gaban sauran mayaƙan a ƙauyen Kajeri Dogumba cikin ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.

Majiyoyin sirri sun gayawa Zagazola Makama cewa Abu Muhammed ya zargi

Abu Darda da jagorantar harin da ba ayi nasara ba a ranar 19 ga watan Maris a Mafa wanda yayi sanadiyyar halaka ƴan ta’addan da dama da kuma ƙwace motocin su guda biyu.

Kwamandan yace motoci uku kawai gare su amma gazawar Abu Darda ta sanya sojojin suka kwace su, inda yayi nuni da cewa ya da suka farmake su suna barci a sansanin.

Kwamandan ya bayyana cewa yaji zafi ne sosai saboda sojojin sun halaka mayaƙan sa da dama, sun ƙona kayan abincinsu da kuma wasu sabbin kayan ɗaki na shirin auren sa da ya siyo.

Kwamandan wanda yanzu haka yake tattaro kan mayaƙan sa a Kajeri Dogumba, Bula Yagana Aliye a ƙaramar hukumar Mafa, ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mayaƙan sa.

Dakarun sojojin Najeriya a Operation Hadin Kai, sun dira a maɓoyar ƴan ta’adda ISWAP a ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar Borno, inda suka halaka ƴan ta’adda 41 ciki har da  wani kwamanda Abu Zahra.

Leave a Reply

%d bloggers like this: