Shugaban kasa Mahammadu Buhari ya kaddamar da aikin fara tonon man fetur a jihar Nassarawa.

Shugaba ya kaddamar da fara tonan man na fetur a karamar hukumar Obi ta jihar Nassarawa

kamar yadda rahoto ke bayyanawa jama a na farin cikin bisa kara samun wata rijiyar da za a kara hakar man.

Ana sa ran cikin kwanaki babban kamfanin man fetur na kasa wato NNPC zai fara hakar man a jihar ta Nassarawa.

A karshen shekarar data gabata ne 2022 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hakar man fetur a Kalmoni da Gombe tsakanin jihohin Bauchi da Gombe Arewacin kasa Najeriya.

Ita dai kasa Najeriya ta dogara da man fetur wanda ake hako mafi yawancin sa daga jihar Delta a kudancin Najeriya.

Sai dai kasar kullum na tunanin yadda za ta karo nemo hanyoyin kudin shigar ta tun da ta dogara da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: