Kungiyar EU mallakin kasashen tarayyar turai ta bayar da nara milliyan 75 don yaki da cutar mashako da ta addabi kasar Najeriya.

Kamar yadda sanarwa ta fito daga kungiyar ta turai EU a jiya litinin bayan taro ta ce ta bayar da euro 150,000 dai-dai da miliyan 75 a kudin kasa Najeriya.
Ta ce za a yi amfani da su wajen magance cutar nan take musamman ma masu hadarin kamuwa da cutar mashako mai rike numfashi.

Kuma za a fi bai wa jihohi kamar Kano, Katsina, Legas, da Osun domin sun fi ko ina kamuwa da cutar mashako.

Kugiyar EU ta ci gaba da cewa za a dauki matakin dakileta sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar ta mashako a farkon shekarar 2023.
Kuma tallafin za a bayar ga mutane akalla sama miliyan daya.
Tallafin dai na zuwa
ne bayan da kungiyar ta fahimci kasa Najeriya na bukatar tallafi game da cutar.
Kuma an tara wadannan kudaden ne sakamakon asusu da aka hada da kungiyoyin Red Cross da Red Croscent don kare aukuwar bala’oi da ke faruwa.