Mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar gwamna a jam”iyyar APC Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya taya zaɓaɓɓen gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf murnar lashe zabe.

Nasiru Gawuna ya aike da sakon taya murna wanda sakataren yada labaransa Hassan Musa Fagge ya aike ga manema labarai.

Dakta Gawuna a cikin saakon taya murnar ya yi bayanin yadda su ka miƙa korafinsu zuwa ga hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC domin ganin an sake zabe a wasu mazabun na jihar Kano.

Sai dai ya ce hukumar ba ta duba kokensu ba yayin da ta mika sakamakon lashe zaɓe ga zaɓaɓɓen gwamnan yau Laraba.

Dakta Nasiru Yusif Gawuna shi ne ya zo naa biyu a zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Mairs din shekarar da mu ke ciki.

Saai dai jamiyyar APC ta nuna rashin gamsuwa da sakaamakon daa hukumar zabe INEC ta ayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: