Wani mutum ya samu mummunan raunin harbin bindiga a lokacin da magoya bayan jam’iyyar APC da PDP suka kaure da fada a Fatakwal ta jihar Ribas a yau Litinin.

tun farko, wasu magoya bayan PDP sun yi zanga-zanga a gaban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta da ke hanyar Aba a birnin na Fatakwal.

Masu zanga-zangar na neman a yi zaman gaba-gadi don duba tare da bincike kan kayayyakin aikin zabe da jam’iyyun siyasa.

Jam’iyyar APC, karkashin jagorancin dan takararta na gwamna a jihar, Tonye Cole a ranar Juma’ar da ta gabata ta ce za ta fito don mamaye ofishin hukumar zabe ta INEC.

A cewar Cole, za a mamaye ofishin na INEC ne domin tabbatar da an sake sahihan takardun aikin zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris don ba APC damar shigar da karar kalubalantar zaben.

Yayin da ‘yan PDP ke zanga-zanga, Cole da shugaban APC na jihar, Emeka Beke da sauran ‘yan APC sun bayyana a ofishin na INEC.

Matasan da ke zanga-zanga sun tunkari inda suke, inda suka yi ta jifan Cole da ‘yan tawgarsa.

Wasu jami’an tsaron da ke tare da Cole sun tafi dashi a mota, inda ‘yan zanga-zangar PDP suka ci gaba da jifa da ledojin ruwa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: