Ɗan majalisa mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume, yace ƴan siyasa sun fara siyan shugabancin majalisa ta 10 wacce ba a kai ga rantsar da ita ba.

Ndume, wanda aka tattauna da shi a gidan talbijin na Channels Tv a shirin su na ‘Sunday Politics’ ya bayyana cewa da yana da kuɗin da zai iya zama shugaban majalisar dattawa a shekarar 2023.

Sanatan na jam’iyyar APC wanda ya kwashe shekara 20 a majalisa, yana son a kafa dokar dukiyar da ba a san yadda aka samo ta ba domin hukunta gurɓatattun ƴan siyasa waɗanda ke da dukiya mai alamar tambaya.

Ya ce yakamata ace akwai dokar nan saboda idan ka nuna dukiya wacce tafi abinda kake samu, sai a bincike ka sannan dukiyar a ƙwace ta kuma idan tayi yawa sosai, sai ka fuskanci tuhuma.

Jam’iyyar APC ta lashe kujeru masu rinjaye na kujerun majalisu a zaɓen inda ta samu kujeru 55 cikin 109 na majalisar dattawa da kujeru 160 cikin 360 na majalisar wakilai.

Jiga-jigan jam’iyyar APC da dama sun nuna aniyar su ta yin takarar shugabancin majalisun biyu.

Daga cikin su akwai Orji Kalu, Jibrin Barau, Godswill Akpabio, Dave Umahi, Ahmad Lawan, Abdulaziz Yari, Osita Izunaso, da sauran su.

Sai dai har ya zuwa yanzu jam’iyyar bata yi magana ba kan shugabancin majalisar.

Shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ya bayyana cewa jam’iyyar bata tsara yankin da shugabannin majalisar zasu fito ba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: