Wasu da ake zargin masu zanga-zanga ne sun shiga ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da karfin tsiya kan cewa sai sun duba naurar zabe a jihar Ribas.

kamar yadda jaridar leadership ta rawito ta ce masu zanga zangar na jamiyar PDP sun shiga INEC bayan sun sako kayan da suke nuna alamun bokaye ne.
Sai dai bayan shigar ta su ne akai yi ta rikici da jami ai akan suna cewa dole sai an bar su sun duba kayyakin da aka gudanar da zabe.

kamar yadda suke cewa suna zargin hukumar zabe ta kasa INEC wajen gudanar da zaben da aka gudanar a jihar ta Ribas akwai kuskure ciki.

ko da yake masu zanga-zangar ba yau Talata suka fara ba tun ranar Litinin inda a yau Talata ne suka shiga ofishin INEC tare tarewa dan takarar jamiiyar APC na gwamna wato Cole hanya inda suka hana shi ya shiga ofishin.
An rawaito cikin masu zanga zangar akwai yan majalisun dokokin jihar dama kakakkin majalissar jihar wanda ya jagoranta.