Gwamnatin jihar Kaduna ta sake tabbatar da mayar da malaman firamare 1,288 da ta kora a shekarar da ta gabata.

Tun a watan Yunin shekarar 2022 gwamnatin ta kori malaman sai dai ta sake mayar daa du tare da yi musu jarrabawa.


Malaman da aka kora sun kai su 2,192 da ba su halarci zaman jarrabawar ba, sai kuma wasu 165 da su ka gaza gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Mia magana da yawun hukumar ilimi daga tushe a jihar Hajiya Mohammed ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta fitar yau a Kaduna.
Ta ce a watan Yunin shekarar 2022 gwamnatin jihar ta kori malaman makarantar firamare 2,357 sakamakon faɗuwa jarrabawar da aka musu.
Wasu daga ciki sun yi ƙorafi cewar ba su da lafiya a lokacin wasu kuwa su ka musanta batun faduwarsu jarrabawar wanda hakan ya sa gwannatin ta sake basu dama tare da sake shirya musu wata jarrabawar.
Bayan sake yin jarrabawar ne kuma gwamnatin ta tabbatar da cancantarsu tare da mayar da su bakin aiki.