Gwamantin jihar Kano ta nada tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa INEC wato Attahiru jega a matsayin shugaban Jami’ar Sa’adatu Rimi.

Kwamishinan yada labarai na jihar Mahammad Garba shi ne ya bayyana haka bayan zaman majalissar zartawar da aka gudanar a fadar gwmantin jihar ta kano.
Garba ya ce gwamnatin ta nada Attahiru Jega a matsayin shugaban makaranatar inda kuma ta nada Uba Mashood zai kasance shugaban majalissar Sa’adatu Rimi.

Ya ci gaba da cewa bayan hukumar jami’oi ta kasa ta amince da jami’ar a matsayin jami’a ta 61 cikin jami’oin kasar 222 da ake da su a Najeriya.

Ya ce gwamnati ta yi la’akari da sashi na 22 na dokar ilimi ta sa’datu Rimi Kumbutso kano.
Sannan akwai sashi na 1 da 2 da 3 na dokar jami’ar wadda ya bai wa gwamna damar yin nadin ga shugaban jami’ar da kuma yan kwamitinsa.
Ya kara da cewa hakan zai sanya bayan shekaru hudu wa’adi ya kare domin kuwa a kara zuwa domin zabar wasu.
Sannan gwamna ya nada wasu mutane da dama daga bangaren na ilimi baya ga shi farfesa.