Gwamnatin Najeriya ta karbi tsabar kudi dala miliyan 800 don rabawa yan kasar don rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Ministar jin kai da walwalar jama’a Hakiya Sadiya Umar Faruk ce ta ayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar zartarwa da aka saba yi mako-mako.

Ta ce magidanta miliyan goma a Najeriya ne za su amfaana da kashin farko na tallafin wanda su ka karba daga bankin duniya.

Kuma za a raba tsabar takardun kudin ne ga magidanta.

Ta ce magidanta miliyan goma da za su bai wa tallafin zai shafi mutane miliyan hamsin na ƙasar.

Sai dai ba ta bayyana nawa za a baai wa kowanne magidanci ba.

Ana sa ran gwamnatin kasar za ta cire tallafin man fetur baki daya a watan Yunin shekarar da mu ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: