Aƙalla mutane 46 aka hallaka a wani sabon hari da aka kai ƙaramar hukumar Otukpo a jihar Benue.

Ko a ranar Talata sai da ƴan bindiga su ka kai hari kauyen Umogidi da ke garin Adoka tare da kashe mutane uku.

Shugaban karamar hukumar Baƙo Eje ya sake tabbatar da kai hari ƙauyen wanda aka hallaka mutane 46 a yammacin Laraba.

Ya ce a yammacin Laraba sai da aka samu gawar mutane 46 sakamakon sabon harin da ƴan bindigan su ka kai yau.

Ya ƙara da cewa an kai harin ne a yammacin ranar Laraba ƙasa da awanni 24 da kai harin da aka hallaka mutane uku.

Tuni aka binne gawarwaki ukun farko da aka hallaka a ranar Talata a cewar Baƙo Eje shugaban karamar hukumar Orukpo a jihar Benue.

Leave a Reply

%d bloggers like this: