Wasu da ake zargin ‘yan Bindiga ne sun hallaka wasu jami’an ‘yan sanda uku tare da raunata daya a lokacin da su ka kai musu hari a Jihar Edo.

 

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 5:30 zuwa 6 na safiya a kusa da babbar kasuwar Agor da ke Jihar.

 

Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a lokacin da jami’an su ke bakin aiki maharan su ka yi musu kwanton ɓauna a kusa da garin na Agor da ke kan hanyar Igarra zuwa Auchi a Jihar.

 

A yayin harin an hallaka dan bindiga daya tare da jikkata wasu daga cikin su.

 

Bayan faruwar lamarin jami’an tsaron sun kwato bindigogi guda shida daga wajen bata-garin.

 

A yayin da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan Jihar Chidi Nwabuzor ya bayyana cewa har kawo yanzu rundunar ba ta samu cikakken bayani akan harin ba , sai dai su na ci gaba da gudanar da bincike akai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: