Wasu ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da tsohon mataimakin gwamnan Jihar Nasarawa Farfesa Onje Gye-wado a Jihar.

‘Yan bindigan sun yi garkuwa da shi ne a gidansa da ke unguwar Gwagi a karamar hukumar Wamba ta Jihar da misalin karfe 12 na daren yau Juma’a.


Daya daga cikin iyalan Onje ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun fasa katangar gidan ne tare da shiga ta dakin matarsa kuma su ka yi awon gaba da shi.
Gye-wado ya kasance mataimakin gwamnan Jihar ta Nasarwa ne tun a shekara ta 1999 zuwa 2003 wanda a baya ya sha tsalle tarkon masu yunkurin yin garkuwa da mutane.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Ramhan Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin.
Nansel ya bayyana cewa bayan faruwar hakan rundunar ƴan sanda hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro a Jihar sun duƙufa wajen kuɓutar da tsohon mataimakin gwamnan.
Kakakin ya yi kira ga al’ummar Jihar da su bai’wa jami’an tsaro bayanai wadda hakan zai kai ga an kuɓutar da shi.