Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta sha alwashin ceto mutanen da aka sace a jihar ba tare da wani ya samesu ba.

Kwamishinna yan sandan jihar Yusuf Kolo ne ya tabbatar da haka a ranar Juma’a bayan fa aka samu rahoton sace wasu yara da mata a ƙauyen Wanzamai da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar.

Daga ciki akwai mata Tara da wasu yara masu yawa.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun ƴan sandan jihar Muhammed Shehu ya sanyawa hannu, sanarwar ta ce jami’an haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro za su hada kai don ganin an kuɓutar da su.

Sannan sun ja hankalin mutane da su kwantar da hankalinsu dangane da faaruwar hakan domin za su ci gaba da aikin tsare rayuka da lafiya da ma dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: