Ƴan bindigan da suka sace mutum 85 a ƙauyen Wanzamai, cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun amince su karɓi N20,000 a matsayin kuɗin fansa kan kowane mutum ɗaya da suka sace.

Ƴan bindigan sun kuma nemi hukumomi da su janye sojojin da aka kai zuwa cikin ƙauyen a cikin sharuɗɗan da suka gindiya domin sakin mutanen da suka sace.

Matashiya tv ta rawaito cewa a ranar Alhamis da ta gabata, ƴan bindigan suka sace kusan kimanin mutum 100 a yankin.

Sun bayar da wa’adin ƙarfe 12:00 na daren ranar Lahadi, inda suka yi barazanar halaka duk wani wanda ba a biya kuɗin fansarsa ba kafin cikar wa’adin da suka bada.

Sun kuma yi barazanar cewa idan dai har ba a janye jami’an sojojin da aka jibge a ƙauyen Wanzamai ba, za su cigaba da sace mutanen ƙauyen.

Wani mazaunin ƙauyen, Abubakar Na’Allah ya gayawa majiyar manema ta wayar tarho cewa ƴan bindiga sun turo saƙo cewa 20,000 kawai za su ƙarba kan kowane mutum ɗaya da suka sace a matsayin kuɗin fansa, duba da cewa talakawa ne marasa ƙarfi a cewarsa.

Na’Allah ya bayyana cewa iyalan waɗanda aka sacen suna ta ƙoƙarin biyan kuɗin inda ya koka kan cewa da yawa daga cikin su, suna ta siyar da abinda suka mallaka domin haɗa kuɗin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: