Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da aikin sanya na’urar tantance matafiya da kayansu a tashoshin jirgin ƙasa.

Karamin ministan sufuri Adegoroye Ademola ne ya tabbatar da haka bayan zaman majalisar zartarwa ta kasa da ta saba gudanarwa mako-mako.
Ya ce aikin sanya na’urorin zai lashe tsabar kuɗi naira miliyan 498.

Za a yi aikin sanya na’urorin ne a tashoshin jirgin ƙasa na Kano, Kaduna da Abuja.

Zamanantar da tsarin sufurin jirgin kasa na daga cikin ayyukan da shugaba Buhari ya sanya a gaba.
Sai dai an samu rahotanni kai wa jiragen kasa hari a lokuta daban-daban.
Sai dai Mista Ademola ya ce hakan zai taimaka wajen ƙara samar da tsaro musamman ga matafiya.