Hukumar jin daɗin alhazai a jihar Kaaduna ta buƙaci ƙarin kujera 500 don bai wa ƴan jihar damar ziyarar aikin hajjin bana.

Babban sakatare a hukumar Dakta Yusif Yaqubu ne ya bayyana buƙatar hakan domin bai wa maniyyata a jihar dama ziyartar ƙasar Saudiyya.

A wani taron manema labarai da hukumar ta shirya ranar Talata, shugaban ya ce hukumar kula da aikin Hajji a Najeriya ta bai wa jihar Kaduna kujera 5,987 da maniyyatan za su biya naira miliyan 2.919 kowanne.

Sannan ya ce kowanne maniyyaci za a ba shi dala 800 kuɗin guziri.

Daakta Alrigasyu ya bayyana dalilin da ya sa aka samu hauhawar farashin kujera a bana, wanda ya ce karin kuɗin haraji, ƙarin kuɗin masauki da hauhawar faarashin dala na daga cikin dalilai da su ka sanya kuɗin kujerar ya tashi.

Sannan ya buga misali da kasashe kaamar Malaysia, Pakistan, Ghana da Nijar wandaa dukkanninsu kuɗin hajjin bana ya haura na Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: