Hukumar ƙidaya a Najeriya NPC ta ɗage ranar fara bayar da horo ga ma’aikatanta a matakin ƙananan hukumomi da masu sanya idanu a kan aikin.

Aa baya, hukumar ta sanya ranar Alhamis 13 ga watan Afrilu domin fara bayar da horo ga ma’aikatan da za su yi aikin ƙidaya a bana.
Daraktan yaɗa labarai a hukumar Dakta Isiaka Yahaya ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafin hukumar na twitter.

Ya ce hukumar na tabbatarwa da ƴan ƙasar cewar sun dukufa domin ganin sun gudanar da ingantaccen aiki na kidayar gidaje da mutane a Najeriya.

Ya ce hukumar za ta sanar da sabuwar da za ta bai wa ma’aikatan horo a nan gaba.
Najeriya ta shafe shekaru 17 ba a yi kidaya ba, kuma hukumar ta ce za a yi aikin har a dajin Sambisa.