Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta tabbatar da cewa ta gano shirin wasu batagari da su ke yunkurin aikata fashi da makami a yankin Apo Zone E Extension da ke birnin na Abuja.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja SP Josephine Ade ta fitar.
Kakakin ta bayyana cewa da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Laraba rundunar ta samu kiran gaggawa daga mutanen yankin na Apo.

Wanda hakan ya sanya jami’an ‘yan sandan da ke tsaka da gudanar da aiki a yankin su ka nufi gurin hakan ya sanya batagarin su ka tsere.

Kakakin ta a ce jami’an sun samu nasarar kama wani mutum daya wanda ake zargi da hannu a cikin aikata ta’addancin.
Rahotanni sun bayyana cewa batagarin sun tsere sun bar kwamfutoci biyu Talabijin uku da kuma wata mota kirar BMW mai lamba ABJ 440 KX.
Amma ana kyautata zaton kayan da mutanen su ka bari na sata ne wanda su ka dauko daga gidajen da su ka shiga.
Kakakin ta ce rundunar tana tsaka da bincike akan wanda su ka kama wanda hakan zai kai da kamo sauran da su ka tsere.