Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin bada gudun mawa ga hukumar kula da yawan jama’a ta kasa a shirye-shiryen da hukumar ke yi na kidayar jama’ar kasar na wannan shekara.

Gwamnan Kano Dr. Abdulahi Umar Ganduje shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin wata ganawa da ‘yan kwamitin hukumar kidaya karkashin jagorancin Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammad suka kaiwa gwamnan a birnin Kano.
Lai Muhammad wanda ya sami wakilcin babban Darakta na hukumar wayar da kai ta kasa Dr. Garba Abari.

Gwamna Ganduje ya bada tabbacin gwamnatinsa nayin aiki tare da hukumar kidaya domin samun nasarar aikin.

Gwamnan ya kara da cewa kidayar zata taimakawa gwamnati musamman hukumar kididdiga ta kasa wajen sanin yawan al’ummar kasar tare da adadin gidaje ta yadda gwamnati zata sami cikakkun bayanai akan duk-kan al’ummar kasar.
Tun da farko a nasa jawabin Ministan Yada labarai da al’adu na kasa ya bayyana cewa an shirya taron ne domin tattaunawa da duk-kan masu ruwa da tsaki domin nasarar shirin kana ya godewa gwaman bisa nada babban mai bashi shawara kan harkar kidaya wanda ya bayyana cewa shine irinsa na farko a tarihi.