Hukumar ba da kariya ga fararen hula ta tabbatar da kame mutum 93 da ake zargi da aikata laifuka tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara.

Babban kwamandan hukumar na Jihar Kano malam Adamu Salihu shine ya tabbatar da hakan a lokacin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a yau juma’a
Adamu ya tabbatar da cewa daga cikin mutanan da hukumar ta kama ta gurfanar da 29 a gaban kotu yayin da ake cigaba da gudanar da bincike akan mutum 57 kafin gurfanar da su a gaban kuliya.

Babban kwamandan ya ba da tabbacin cewar hukumar na cigaba da gudanar da aiki kamar yadda doka ta tanada, na bada kariya ga al’umma.

Adamu Salihu ya kuma bukaci hadin kan al’umma da su zamto masu bawa jami’an tsaro hadin kai tare da bayanai domin a cewarsa al’amarin tsaro ya shafi kowa da kowa ne ba iya jami’an tsaro ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: