Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatara da kubutar da mutum 11 da aka yi garkuwa da su a kauyen Kucheri da ke yankin karamar hukumar Tsafe ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar CSP Muhammad Shehu shine ya tabbatar da hakan a safiyar yau a Gusau babban birnin jihar.

Shehu ya bayyana cewa 2 daga cikin mutanan maza ne yayin da 7 suka kasance mata.

cigaba duba lafiyar mutanan a asibiitin ‘yan sanda da ke Gusaua kana za’a sada mutanan da Iyalansu nan ba da jimawa ba.

CSP Muhammad Shehu ya bada tabbacin rundunar ‘yan sandan jihar na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da kawo karshen ta’addanci a fadin jihar.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kara da cewa nasarar da jami’an nasu suka samu tana da nasaba da hadin kan da al’umma ke baiwa jami’an tsaro da kuma bayanan sirri da rundunar ke samu daga al’ummar jihar.

Kakakin ya kuma tabbatar da cewa ana

Leave a Reply

%d bloggers like this: