Yan sanda sun kashe wasu mutum uku da ake zargin ’yan bindiga ne a Karamar Hukumar Lafiya ta Jihar Nasarawa.

An kashe wadanda ake zargin ne yayin wani artabu da suka da jami’an ‘yan sandan jihar a ranar Juma’a.


A yayin arangamar, an ceto wani mutum da suka sace mai suna, Ezekiel Luka – daga Jihar Taraba, sa’o’i 24 bayan sace shi.
Kakakin ‘yan sandan Jihar, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a.
Nansel, ya ce jami’an ‘yan sandan sun samu bayanai a ranar Alhamis cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare hanyar Assakio-Sabon Gida.
Ya ce a ranar 13 ga watan Afirlu 2023, an samu labarin cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare hanyar Assakio-Sabon Gida da ke yankin Lafia, inda suka yi garkuwa da wani mutum mai suna Ezekiel Luka dan asalin Jihar Taraba.
Ya ce an kama wani da ake zargin dan bindiga ne da wata bindiga mai dauke da harsashi bakwai a cikint.