Jam’iyyar APC ta ci gaba da zama mafi rinjaye a majalisar wakilai ta Najeriya, inda ta samu mafi yawan kujerun majalisa a zaben bana da aka kammala.

Har yanzu, ana ci gaba da sanar da sakamakon zaben majalisar wakilai ta kasa da ake karasawa a zaben cike gurbin da aka gudanar ranar Asabar 15 ga watan Afrilu.

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta jagoranci gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Faburairu.

Sai dai, an samu tsaiko a lokacin zaben, wanda hakan ya sanya aka dage shi a wasu yankuna tare da sanar da ranar zaben cike gurbi a matsayin 15 ga Afrilu.

Bayan zaben 25 ga watan Faburairu, shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya sanar da cewa, an kammala zaben majalisar kasa na kujeru 423 cikin 469, kuma an sanar da sakamakonsu.

A cewarsa, daga ciki, an sanar da 325 na majalisar wakilai daga 360, yayin da sauran kuma suka kasance na sanatoci a kasar.

A cewar Farfesa Yakubu, a majalisar wakilai ta kasa, APC ta samu kujeru 162 yayin da jam’iyyar PDP kuma ta samu kujeru 102.

Ya kara da cewa, jam’iyyar Labour da NNPP ta su Kwankwaso sun samu kujeru 34 da 18 bi da bi, APGA ta samu hudu, sai kuma ADC da SDP masu kujeru biyu kowanne da kuma YPP mai kujera daya tak.

A tun farko, INEC ta ce za a gudanar zaben cike girbin ne a mazabu 46 na kasar nan don cike zaben ‘yan majalisun wakilai na tarayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: