Wata kotu dake zamanta a unguwar rijiyar zaki a kano ta zauna domin saurar karar da aka shigar gabanta kan zargin mawakin siyasa Dauda kahutu rarara miliyan Goma.

Zaman kotun da aka yi mawaki dauda kahutu Rarara ta bakin lauyansa ya ce wannan tuhumar da ake yiwa Rarara akan yin kasuwanci da wani mutum mai suna Mahammad Ma’aji wanda Rarara ya hana shi kudin kasuwancin da suka yi ba gaskiya ba ne.

Kamar yadda mai shigar da kara ya bayyanawa kotu ya ce sun yi wani kasuwanci da mawakin tun shekarar 2021 amma rara ya hana shi kudinsa karshe ma ya na cewa bai san an yi ba.

Sannan masu karar sun bayyana cewa suna da na su hujojin a rubuce kuma tuni suka mika su ga mai shari a Halhalatu Kuza’i Zakariyya.

Halhalatul Kuza’i ya dage shariar zuwa wani lokaci domin sake dawo zaman kotun.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: