Gamayyar ƙungiyoyin da ke sha’awar tsoma baƙi a harkokin siyasa a arewa maso yamma, ‘Rescue North West APC Group’ ta ce ta raba gardama kan kujerar shugaban majalisar dattawa.

Jaridar Punch ta ruwaito gamayyar ƙungiyoyin na cewa shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ce ta cancanta ta samu kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10 da za’a kafa.


A cewarsu, ya kamata a baiwa shiyyar wannan kujera saboda ta ba da gudummuwar tulin ƙuri’u, waɗanda suka taimaki zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya kai ga nasara a zaɓen 2023.
Bayan taron da ƙungiyoyin suka gudanar a jihohin Katsina, Kaduna, Kano, Jigawa, Kebbi da Sakkwato, sun cimma matsayar goyon bayan Sanata Barau Jibrin.
Wannan matsaya na ƙunshe a wata sanarwa da Kodinetan gamayyar ƙungiyoyin, Muktar Dahiru-Gore, ya rabawa manema labarai ranar Laraba.