Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta musanta zargin cewa wasu jami’an ta sun haɗa baki da gwamnatin jihar Adamawa domin yin maguɗi a zaɓen gwamnan jihar.

Manema labarai sun kawo rahoto cewa, an yi zargin cewa wasu daga cikin jami’an hukumar INEC sun ziyarci fadar gwamnatin jihar cikin tsakar dare, domin kitsa yadda za a taimaka a yi wa gwamna mai ci Ahmadu Fintiri, maguɗi ya cinye zaɓen.


A wata sanarwa da kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin watsa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Festus Okoye, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce ko kaɗan jami’an hukumar ba su ziyarci gidan gwamnatin ba kafin zaɓen cike gurbin gwamnan jihar na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.
Okoye ya yi nuni da cewa hukumar baturen zaɓe ɗaya kawai ta naɗa domin zaɓen gwamnan jihar, wanda kuma shine ya zama baturen zaɓen jihar na zaɓen shugaban ƙasa.
Ya kara da cewa kamar sauran baturen zaɓe na ƙasar nan, shi ma hukumar INEC ta ba shi takardar aiki, kuma sai da aka sanar da kwamishinan zaɓen INEC na jihar.
Haka kuma jerin sunayen jami’an tattara sakamakon zaɓen tuni aka tura shi zuwa jihar, inda shugaban INEC da kan shi ya sanya hannu a kowane shafi na jerin sunayen, tun kafin isar kwamishinonin INEC da za su yi aikin sa ido a kan zaɓen.