Social Media ko Online Media?
Jaridar Yanar Gizo ko Dandalin Sa Da Zumunta?
Ɗan Jarida ko Ɗaan Social Media?
Assalamu alaikum, na ga dacewar na yi wannan rubutu ne domin fahimtar da ƴan uwa a kan ma’anar waɗannan sunaye guda biyu da ke da muhimmanci da tasiri a rayuwarmu tare da ayyukansu.
Kasancewar zamani ya zo da mutane da dama ke amfani da kafafen sa da zumunta (Social Network Site), wanda a fassarar da aka yi masa ake kira (Dandalin Sa Da Zumunta Na Kimiyya Da Fasahar Sadarwa).
Wasu mutanen su kan kasa bambance abubuwan guda biyu.
Zan fara da na farko wato Online Media.
Online Media, kafar yaɗa labarai ce, ko in ce gidan jarida, wanda ya ke aike da saƙon bayanai ga al’umma ta kafofin sadarwar zamani kamar yadda na fassara a baya.
Sun kasu kasu daban-daban kamar yadda a kafofin yaɗa labarai su akwai Rediyo, Talabiji da kuma Jarida, haka zalika akwai Rediyo, Talabiji, da Jarida da ake watsa labarai a yanar gizo.
A ƙa’ida, ana iya yi wa irin waɗannan kafafen yaɗa labarai rijista kamar yadda hukumomi masu kula da rijistar kamfanoni ke yi a Najeriya da sauran ƙasashe, sannan sun a yin aikin su kamar waɗancan da mu ka sani a baya wanda a turamci ake kira (Conventional).
Ayyukansu na da tasiri matuƙa musamman masu talabiji na yanar gizo kasancewar ko mutum bai je makaranta ba zai iya fahimtar saƙon saɓanin na rubutu da ake karanta.
Haka abin yake a ɓangaren rediyon yanar gizo, sai dai ba ta da farin jini kamar talabiji ganin yadda talabijin ta fara shiga zukantan mutane tun da farko.
Ma’aikatan da ke aiki a irin waɗannan kafofin watsa labarai na yanar gizo ƴan jarida ne cikakku da ked a gogewa da horo daban-daban a aikin jarida kuma su ke kula da ƙaidar aikin jarida.
Ana karantar aikin jarida na yanar gizo a makarantun kwaleji, jami’a da sauran wuraren bayar da horon aikin jarida kuma ana kiran darasin da suna (Online Media).
Kasancewar duniyar ta koma yanar gizo a yanzu ya sa sauran kafofin watsa labarai kamar Rediyo da Talabiji da Jaridu wanda su ke Conventional, su ma su kan buɗe irin waɗannan kafofi domin watsa labarai da sauran ayyukansu.
Misalai na wuraren da ake watsa labarai ko yin aikin jarida a a yanar gizo.
Internet (www)
YouTube
Facebook
Twitter
Instagram
Whatsapp
TikTok da sauransu.

Wannan a taƙaice ke nan.
To mu kalli waccen kalma ta Social Media, ko kuma mu ce ɗan Social Media.
Social media da aka sani kalma ce ta turamci wadda kusan kowa ya san me ake nufi da haka, kuma ma’anar na fassarata, to su wanene ƴan Social Media?
Ƴan social Media sun kasu kashi daban-daban kasantuwar damar da kusan kowa ke da ita na samun damar buɗewa.
Akwai waɗanda su ke buɗewa domin kasuwanci, karatu, tallata manufa, wayar da kai, da kuma masu ƴan jarida na boge, siyasa, Ƴan damfara na fili da na ɓoye da sauransu.
Zan fara da ƴan jarida na boge, mutane ne da ke kwaikwayon aikin jarida ba tare da sun koya ko sun karanta ba.
Ana iya ganesu ta yadda su ke saka abu, ko na batsa, ko ƙarya ko kuma wani abu da ya danganci cin zarafi wanda dukka sun saɓa da ƙa’idar aikin jarida.
Masu talla, mu na yin amfani da kafofin ne domin tallata haja, kasuwancin siye da siyarwa da kuma saka irin kayan da su ke siyarwa.
Wayar da kai, mutane ne da su ke buɗe kafofin sa da zumunta domin sanar da wani ilimi ta yadda za su wayar da kan al’umma ko faɗakar da su, amma su ma ba ƴan jarida ba ne.
Siyasa, mutane da ke saka ayyukansu domin tallata siyasa, ko kuma buɗe shafin wani fitaccen ɗan siyasa yadda zai dinga isar da saƙonsa kai tsaye zuwa ga al’umma.
Tallata manufa, ya kasu kashi-kashi domin akwai masu tallata addini, Tawaye, da wasu abubuwa da za su ja hankali ko tara mabiya.
Ƴan damfara na fili (bambaɗanci/Maroƙa/Ƴan neman fada), yadda su ke tasu damfarar da yaudarar ita ce, za su dinga yin rubutu a kanka ko saka hotonka a kai a kai yayin da kake da kuɗi, muƙami, mulki ko wani abu da za su raɓu da kai don su moreka, yadda za ka gane ƴan damfara ne, da zarar damar da kake da ita ta kuɓuce, za ka nemesu ka rasa.
Ƴan damfara na ɓoye, su kuma su na iya amfani da hoto ko sunan wani fitacce ko mace don jan ra’ayi tare da amfani da buƙatar da su ke so wajen yin damfara.
Wannan shi ne abin da nag a dacewar fahimtar da mu don mu ankare, na san mai karatu za ka iya bambancewa tsakanin Jaridar Yanar Gizo da Ƴan Yanar Gizo.
Allah ya sa mu dace amin.
© Abubakar Murtala Ibrahim
#Abbanmatashiya
Litinin
4 Shauwal 1444
24/4/2023

