Yayin da ake ta kai-komo kan wadanda za su zama shugabannin majalisa, rahotanni na nuna yuwuwar Asiwaju Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya.

 

Jaridar Punch ta ce akwai yiwuwar jirgin Asiwaju Bola Tinubu wanda shi ne shugaban kasa mai jiran gado, ya sauka a kasar nan a yau Litinin.

 

Dawowar zababben shugaban zai ba shi damar samun ta-cewa kan yadda siyasa take tafiya.

 

Hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan majalisar gudanarwa wato NWC na jam’iyyar APC suke kokarin yin zama kan zaben majalisar tarayya.

 

Majalisar NWC za tayi kokarin gujewa abin da ya faru a shekarar 2015 da Bukola Saraki da Yakubu Dogara suka zama shugabanni ba don son jam’iyyar APC ba.

 

Tun a watan Maris Bola Tinubu ya bar Najeriya zuwa Faransa da Ingila, har yanzu bai dawo ba, a wancan lokacin ya bar kasar ne domin ya samu hutu.

 

Sakataren kwamitin yakin neman zaben Shugaban kasa, James Faleke ya yi magana a shafin Twitter, yake cewa a yau Litinin Tinubu zai dawogida Najeriya bayan shafe kwanaki a ziyararsa ƙasashen ketare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: