Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa aikin shimfida bututun iskar gas wanda ake yi daga Ajakuta zuwa kano bai dakata ba.

kamar yadda Malam Mele Kolo Kyari ya bayyana ya ce aikin ana anan ana ci gaba da gudanarwa kamar yadda aka fara.
Ya ce yanzu haka gwamnatin tarayya ta barnata kudade kimanin da dala bilyan daya a yayin aikin.

Kuma tuni aikin yayi nisa sosai tun lokacin da aka fara yin sa.

Ya ci gabada cewa babu wani dan kwangilar da yake bin wasu kudade a yanzu haka don kuwa an biya kowa kudin aikinsa.
Sannan ya ci gaba da cewa ikirarin da wasu mutane ke cewa an dakatar da aikin, ba gaskiya ba ne domin ana ci gaba da aiki ba dare ba rana.
Ya kara da cewa aikin sanya bututun iskar gas zai kawo babban ci gaba ga alummar kasar domin amfanin ga kasa baki daya.
sai dai wasu daga cikin aulmmar kasar sun bayyana cewa aikin ba zai yuwu ba domin girmansa, wanda kyari ya ce wannan aiki an sanya masa lokuta kadan domin kammalawa