Gwamnatin jihar Benue ta lissafo dalilan ta na ganin cewa bai kamata a gudanar da ƙidayar shekarar 2023 a cikin watan Mayu ba.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), a ranar Talata tace mutane da ƙauyuka da yawa ba za a ƙirga su ba idan aka gudanar da aikin kamar yadda aka tsara.
Ko a makonnin da suka gabata, sai da gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya roƙi gwamnatin tarayya da ta ɗaga ƙidayar har sai ƴan gudun hijira a jihar Benue da sauran jihohin ƙasar nan sun koma gidajen su.

Babban sakataren hukumar SEMA, Dr. Emmanuel Shior, wanda ya ƙara jaddada wannan kiran na a dakatar da ƙidayar, yayin da yake tattaunawa da ƴan jarida a birnin Makurdi, ya ce ya kamata a ɗage aikin domin kada mutane da dama a kasa ƙirga su.

Sanarwar tace suna kira da a dakatar da ƙidaya a yanzu saboda suna zargin cewa idan gwamnatin tarayya ta ci gaba da shirin, mutane da dama ba za a ƙidaya su saboda ba za a je gidajen su da ƙauyukan su ba.