Hukumar shirya jarabawan shiga manyan makarantun gaba da Sakandire (JAMB) ta fara jarabawar bana UTME 2023 a faɗin Najeriya.

Bayanan da suka fito daga JAMB sun nuna cewa ɗalibai kusan miliyan 1.6m ne zasu zauna jarabawar bana a faɗin Cibiyoyin rubuta JAMB sama da 700.

Haka nan jadawalin ya nuna za’a kammala jarabawar ranar 12 ga watan Mayu, 2023 domin ba da damar fara jarabawar Direct Entry watau D.E.

Wakilin jaridar Punch ya ziyarci wasu daga cikin cibiyoyin rubuta jarabawar JAMB a Ilorin, babban birnin jihar Kwara da ke arewa ta tsakiya a Najeriya.

Yayin wannan ziyara ya gano cewa jami’an hukumar JAMB na tantance kowane ɗalibi da na’urar gane shacin yatsa gabanin shiga ɗakin rubuta jarabawar.

Sai dai wasu daga cikin masu zuwa zama jarabawar sun koka kan matsalolin da ake samu yayin tantance su, lamarin da wasu jami’an hukumar suka shaida cewa za’a warware nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: