Ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa Aishat Dahiru Ahmed ta janye karar da ta shigar da hukumar INEC a gaban kotu.

 

 

 

Ƴar takarar wadda aka fi sani da Aisha Binani ta janye kaarar da ta shigar gaaban hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC reshen jihar Adamawa har take bukatar kotu ta duba ayyanata a matsayin wadda ta lashe zaɓe tun da farko.

 

 

 

Gamayyar lauyoyin Binani ƙarƙashin jagorancin Mohammed Sherrif sun buƙaci kotu ta janye ƙarar d asu ke yi a kan INEC daga cikin kararrakin da su ka shigar gabanta.

 

 

 

An shigar da karar a babban kotun tarayya karkashin mai shari’a Inyang Ekwo.

 

 

 

Daga ƙarshe kotun ta kori dukkan kararrakin da Binani ta shigar gabanta wadda ke iƙirarin lashe zaben gwamnan jihar.

 

 

 

Tun da farko, tsohon shugaban hukumar zabe a jihar ya ayyana Asiha Binani a matsayin wadda ta lashe zabe.

 

 

 

Sai dai hukumar ta soke karɓar sakamakon sakamakon yadda aka gano akwai sauran kananan hukumomin da ba a gaabatar da sakamakon su ba.

 

 

 

Daga karshe bayan kaammala tattara sakamakon zaben hukumar ta ayyana Ahmad Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna karo na biyu a Adamawa

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: