Gamayyar kungiyoyin jam’iyyar APC a shiyyar kudu maso yamma sun goyi bayan Sanata Musa Sani don jagorantar majalisar dattawan ƙasar karo na goma.

 

Sanata Musa Sani shi ke wakiltar Neja ta gabas a jihar Neja.

 

Koodinetan kmgamayyar kungiyoyin Ade Ifeshile ne ya bayyana haka yau, ya ce cancanta ce ta sa su ka goyi bayan Sanata Sani Musa don jagorantar majalisar.

 

Ya kara da cewa dattakon da Sanata Musa Sani ya yi na janyewa daga neman shugabancin ƙungiyar a shekarar 2022 na daaga cikin dalilan da su ka duba.

 

Sanarwar ta ce tsayar da Sanata Sani Musa zai karawa majalisar kima da daraja.

 

Gamayyar Ƙungiyoyin sun aike da takarda ga Sanata Sani Musa tare da nuna goyon bayansa don jagorantar majalisar.

 

Ana ta dambarwa a kan tunanin wanda zai gaji kujerar majalisar dattawa yayin da jam”iyyar APC ke da mafi rinjayen yan majalisa a zauren.

Leave a Reply

%d bloggers like this: