Hukumar jin daɗin alhazai a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ta sanya ranar 5 ga watan Mayu domin fara duba lafiyar maniyyata.

 

 

 

Hukumar ta sanya ranar 7 ga watan Mayu domin kammala duba lafiyar maniyyatan baki ɗaya.

 

 

 

Daraktan hukumar Malam Abubakar ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ya sanyawa hannu.

 

 

 

Za a faara yi wa maniyyata riga-kafin daga ranar 15 ga watan Mayu zuwa ranar 17 ga watan.

 

 

 

Hukumar ta shawarci maniyyata da su tabbatar sun bi dukkan dokoki da sharudan da aka saka don samun gudanar da aikin hajji a bana.

 

 

 

Sannan sun gargadi waɗanda har yanzu ba su mayar da fom dinsu ba don ganin sun hanzarta yadda za su samu fasfo dinsu na tafiya.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: