Hukumar bada kariya ga fararen hula NSCDC ta bayyana cewa ta aike da jami’anta 422 zuwa cibiyoyin rubuta jarabawar shiga jami’a 37 na jihar Kano.

Babban kwamandan hukumar na jihar Kano malam Adamu Salihu shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a birnin Kano.

Adamu ya bayyana cewa sun aike da jami’an nasu ne domin duba yadda jarabawar ke gudana a fadin jihar tare da bada cikakken tsaro a cibiyoyin rubuta jarabawar.

Ya kara da cewa an aike da jami’ai biyu ga dukkan cibiyoyin rubuta jarabawar a fadin jihar Kano. Wakilinmu da ya duba yadda jarabawar ke gudana ya rawaito cewa jarabawar na gudana cikin lumana da kwanciyar hankali.

Ana saran kimanin dalibai miliyan daya da dubu dari biyar ne zasu rubuta jarrabawar a fadin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: