Jami’an hukumar hisba da ke Jihar Kebbi sun kama wasu yara maza da Mata 12 masu kananan shekaru dake aikata badala a wani Hotel da ke birnin Kebbi.

Kwamanadan hukumar Ustaz Sulaiman Muhammad shine ya tabbatar da kamen a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Jihar.

Ustaz Sulaiman ya ce mutanen da suka kama sun hada da maza Takwas Mata hudu kuma dukkannin su Sun amsa laifukan da ake tuhumar su da shi.

Kwamandan ya ja kunne masu gidajen hotel da su guji Bai wa yara masu kananan shekaru dakuna domin aikata badala.

Sannan ya kara da cewa tuni su ka mika yaran ga iyayen su tare da alkawarin cewa ba zasu sake aikata hakan ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: