Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa jirgin farko na ‘yan Najeriya da yaki ya rutsa dasu a kasar Sudan za su iso gida Najeriya a yau Juma’a.

Shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewa ana sa ran mutane 1500 jirgin Air Peace zai kwaso su daga kasar Masar a yau Juma’a zuwa birnin tarayya Abuja.

A yayin wani taro da aka gudanar a ranar Alhamis mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa NEMA Ezekiel Manzo ya tabbatar da cewa jirgin farko zai fara sauka a ranar Juma’a a birnin na Abuja.

Kakakin ya bayyana cewa a yayin kwaso mutanen za a fi bayar da fifiko ga mata da kananan yara da Dalibai daga cikin ‘yan Najeriya miliyan uku da ke kasar ta Sudan.

Abike ta ce manyan motocin Bas 13 tuni su ka isa iyakar kasar Masar da ke Aswan inda jakadan Najeriya da Darakta-Janar na hukumar NEMA za su tarbi motocin.

Shugabar ta bayyana hakan ne ta cikin wata hira da aka yi da ita a gidan Talabijin na Channels TV ta ce wasu jami’o’i a Najeriya sun nuna sha’awar daukar daliban da suka dawo daga Kasar ta Sudan domin ci gaba da karatun su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: