Akalla mutane 14 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin mota da ya afku a Jihar Bauchi.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:17 na ranar Alhamis a kauyen Zangoro da ke Bauchi Darazo a Jihar.
Kwamanda a hukumar kiyayye afkuwar hadurra ta Jihar FRSC Mr Yusuf Abdullahi shine ya tabbatar da faruwar lamarin.

Mr Yusuf ya bayyana cewa a yayin hadarin mutane biyar sun jikkata inda aka aike da su Asibiti domin kula da lafiyar su.

Kwamanadan ya ce hadarin ya faru ne a tsakanin wasu motoci guda biyu a lokacin da suke gudun wuce sa’a.
Sannan ya ce a yayin kaiwa mutanan dauki jami’an hukumar sun gano kudi naira73.000 da wayoyin hannu guda bakwai jakunkunan hannu hudu da kuma batirin chajin waya daya.
Kwamandan ya kara da cewa an kai gawarwakin wadanda su ka rasa rayukansu Asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa domin gudanar da bincike akansu.
Daga karshe Yusuf ya gargadi masu ababan hawa da su rage gudun wuce sa’a domin kaucewa yawaitar afkuwar hadurra.