Wasu jiragen yakin jami’an sojin kasar Amurka biyu sunyi karo da juna a wani atisayen koyan tuki da suke gudanarwa a birnin Alaska na kasar.

Rundunar sojin Kasar ta bayyana cewa hadarin ya faru ne a ranar Alhamis, inda ta ce hadarin irinsa na biyu kenan da faru cikin kasa da wata daya a Kasar.
A wata sanarwa da bataliya ta 11 Airborne division da ke kasar ta fitar ta ce jiragen masu saukar ungulu su na kan hanyar su ne ta dawowa daga atisayen koyan tuki inda kowanne jirgi ke dauke da mutum biyu a ciki.

Sanarwar ta ce jami’an soji uku ne su ka rasa rayukansu guda ya jikkata.

Idan ba a manta ba koda a karshen watan Maris din da ya kare saida wasu jirage masu saukar ungulu a kasar ta Amurka su kayi hadari wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane Tara dake cikin jirgin.