Gwamnatin ƙasar Masar ta amince tare da buɗe iyakar kasarta da Sudan domin bai wa ƴan Najeriya da ke neman mafaka a ciki.

Hakan ya biyo baayan ci gaba da kai hare-hare da aka ci gaba d ayi a babban birnin kasar Sudan.
Gwmanatin Najeriya ta ce ta kase tsabar kuɗi sama da dala biliyan ɗaya domin kwaso yan Najeriya da ke karatu a kasar.

Batun da mutane ke ta cece ku ce a kai taare da ganin an kashe kuɗaɗe da yawa a kai.

Tun a makon da ya gabata gwamnatin ta ce ta fara jigilar mutanen da ta shirya kwasowa sama da dubu biyu.
A baya, gwamnatin ƙasar Masaar sun ki amincewa da bude iyakar kasar domin shigar yan Najeriyaa.
Sai da daga baya sun amince bayan shugaba Muhammadu Buhari ya tsoma baki a kai.