Rundunar yan sandan Najeriya ta tabbatar da kama tsohon kwamishinan zaben jihar Adamawa.

An kama Barista Yunusa Ari bayan buƙatar hakan daga hukumar zaɓe a Najeriya INEC ta aikewa sufeton ƴan sanda na ƙasa.
Mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya Muyiwa Adejobi ne ya sanar da haka tare da tabbatar da kamun yau Talata.

Ya ce wasu daga cikin mutanen da ake zargi da hanu wajen kawo cikas a zaben su ma sun shiga hannu.

Yunusa Ari ya shiga zargi bayan ayyana Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa.
Hukumar zaben ta dakatar da karɓar sakamakon wanda ta ce hakan bai dace da tsarin ba.
An yi zargin tsohon shugaban ya ayyana sakamakon kafin karɓar sakamakon zaɓen wasu kananan hukumomi a jihar.