Gwamnati tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta cefanar da babban asibitin fadar shugaban kasa na Aso Rock.

Sakataren gwamnatin tarayyyane daga fadar shugaban kasa ya bayyana hakan bayan zaman da hukumar ICRC ta shirya a jiya.


Cikin sanarwar ta ce za a siyar da Asibitin fadar shugaban kasa sakamakon rashin kudi da kasar ke fama da kuma bijiro da wasu hanyoyin samun kudi.
Sannan kuma akwai wasu Karin abubuwa da za a siyar kamar yankunan gandun daji na bude idon yara da kuma dakin Shan magani wanda yake a jihar Legas.
Sannan ya ce gwamnati za ta yi hakkanne domin samun kulawa da abubuwan da za su dinga samu musamman Asibitin.
Ko da a kwanakin baya sai da gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan takwas da rabi domin gyara asibitin fadar shugaban kasa dake Aso Rock babban birnin tarrayyar Abuja.