Tsohon shugaban hukumar kiddiga ta kasa Najeriya NBA Mr. Okey Wali ya shaki iskar yanci daga hannun yan garkuwa da mutane.

Kamar yadda wata sanarwa ta bayyana ta ce an yi garkuwa da shugaban hukumar kiddiga ta kasa makonni biyu da suka gaba ta.


Kuma yanzu haka an jada shi da iyalansa bayan shakar iskar yanci.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana cewa ko ambiya kudi ba kafin sakinsa ko akasin haka.
A ranar 17 ga watan Afirilu ne dai wasu da ake zargin yan garkuwa suka shiga unguwar Obio dake karamar hukumar Akpio inda suka afka gidansa Okey Wali tare tafiya da shi har yayi tsawon kwanaki 14 a wurinsu a jihar Ribas.
Sai dai ba a ji matsayar hukumar yan sandan jihar Ribas ba dangane da haka.
Matsalar garkuwa a kasa irin Najeriya ta zama ruwan dare inda baga manyan kasar ba ko kanana dukda gwamnati mai barin gado ta ce ta magance matsalar.