Wata kungiyar siyasa a Arewacin Najeriya ta amince da bai wa tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari goyon baya a matsayin shugaban majalisar dattawa ta goma.

Ƙungiyar mai suna ‘The North-West Progressives Forum’ ta gargadi zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu da kada ya kuskura ya ba da dama ga sauran yankunan kasar na shugabancin majalisar.

Shugaban kungiyar, Nasir Danbatta da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a ranar Asabar 29 ga watan Afrilu, yace arewa maso yammacin kasar tafi kowane yanki ba da ƙuri’u ga jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa da ya gabata.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kungiyar da ke arewa maso yamma tace babu wanda ya cancanci kujerar majalisar dattawa kamar tsohon gwamnan jihar Zamfara.

Ta kuma gargadi zababben shugaban kasar Najeriya da ya tabbatar ya bai wa Abdulaziz Yari domin yankinsa ya ba da kaso mafi tsoka a cikin kuri’un da aka kada.

Kungiyar tace rashin adalci ne kawai zai sa a bai wa wani yanki na kasar nan shugabancin kujerar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: